July 16, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Za’a bude sufurin tashin jiragen – kasa da kasa

1 min read

Ministan harkokin sufurin sama,
Hadi Sirika ya musanta matakin fara zirga-zirgar
jiragen kasa-da-kasa a watan Oktoba kamar yadda
jaridun kasar suka rawaito.
Ya bayyana cewa zasu bayyana lokacin da suka tsara
fara fita da jirage.
Sirika ya bayyana hakan ne a wani sakon da ya wallafa
a shafinsa na Twitter inda ya kara da cewa wata kila
ma a fara zirga-zirgar jiragen kafin watan Oktoba.
Hakan na nufin cewa jirage masu aiki na musamman
da na jami’an difilomasiyya ne kadai aka baiwa dama a
halin yanzu, har sai an tabbatar da lokacin bude zirga-
zirgar kasa-da-kasa.
A cikin watan Maris din da ya gabata ne gwamnatin
Najeriya ta dakatar da zirga-zirgar jiragen kasa-da-kasa
domin dakile yaduwar cutar Coronavirus.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *