June 13, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

An kama wani Babban Dan Sanda da ya dade yana bunsuranci da wata a amarya a nan Kano.

1 min read

Ana zargin wani Dan sanda da yiwa wata Amarya kartanci.
Dan sandan dai ya ringa shiga gidan wani mutum yana tsallaka masa iyaka a karamar hukumar Wudil dake nan Kano.

Tin asali dai Mijin amaryan yana da Mata uku ne dalilin da ya sanya shi raba kwana kuma kowacce gidanta daban, wannan dalilin ne ya sanya dan sandan ke amfani da Ranakun da mijin amaryar baya gidan amaryar domin gudanar da Bunsuranci a gidan.

Magidancin yayi amfani da makota wajen kama wannan dan sanda domin gurfanar dashi gaban hukuma.

DSP Abdullahi Haruna Kiyawa shi ne Jami’in Hulda da jama’a na Rundunar ‘Yan sandan Jihar Kano,Ya ce tini suka kama wannan dan sanda tare da Amaryar domin tsawaita bincike akai.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *