June 13, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

An kama wasu masu garkuwa da mutane a

1 min read

Rundunar ‘yan-sandan Jihar Kaduna ta ce, ta kama wadanda ta ke zargin aikata laifuka daban-daban ciki har da masu yin garkuwa da mutane da masu satan shanu da masu ta da zaune tsaye dari biyu da goma sha Bakwai.
Kwamishina ‘yan sandan na jihar Malam Umar Muri ne ya tabbatar da hakan yayin zantawa da manema labarai.
A cewar kwamishinan Umar Muri suna zargin wadancan mutanen ne da aikta manyan laifuka tsakanin watan Afrilun zuwa watan Yuli bana.
A cewar sa, sun kuma kwace muggan makamai har Arba’in da uku wadanda tuni ya bada umarnin kai su inda ba wanda zai gansu kafin rundunar ta yanke hukunci akan su.
Kwamshinan ya kira ga la’umma da su ci gaba ba su hadin kai don kawo karshen ta’andanci a fadin kasar nan.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *