September 22, 2023

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Babu ministan da ‘ya fi ƙarfin majalisar dokokin Najeriya’

2 min read

Shugaban majalisar dattawan Najeriya Ahmad Lawan ya ce babu wani
mutum da ke karkashin gwamnati da ya fi karfin majalisar dokokin
kasar ta gayyace shi domin ya amsa tambayoyi.
Ahmad Lawan ya bayyana haka ne a zaman majalisar da aka gudanar
ranar Alhamis.
A sakon da ya wallafa a Twitter, Sanata Lawan ya ce: “lokacin da muke
tashi daga zaman majalisa na jiya na yi magana kan bukatar da ke
akwai ga mutanen da shugaban kasa ya nada kan mukamai su guji ce-
ce-ku-ce na babu gaira babu dalili da kwamitocin majalisun dokoki
domin kuwa babu wanda ya wuce majalisa ta yi bincike a kansa.”
Ya kara da cewa kwamitocin majalisar suna gayyatar hukumomin
gwamnati ne domin gudanar da ayyukan da al’umma suka aike su
majalisun su yi kamar yadda tsarin mulkin shekarar 1999 ya gindaya.
A baya bayan nan dai ana samun takun saka tsakanin ministoci da ‘yan
majalisa, inda ko a makon da muke ciki sai da ministan yankin Naija
Delta Godswill Akpabio ya yi zargin cewa ‘ A farkon watan nan, minista a ma’aikatar kwadago ya kai ruwa rana da
‘yan majalisar game da zargin tsoma bakinsu a kan shirin shugaban
kasar na bai wa matasa aikin yi wanda aka fi sani da N-Power.
Masu lura da lamura na ganin wannan takaddama d ke tsakanin
bangarorin biyu abin kunya ne ganin cewa ‘yan majalisar da bangaren
zartarwa abokan juna ne ta fannin siyasa, sabanin majalisar da ta
gabace ta, wacce ake ganin ta hana ruwa gudu a gwamnatin Shugaba
Buhari.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *