September 22, 2023

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Gobara ta kone tashar Tv ta NTA

1 min read

Wasu bangarori uku a tashar gidan telebijon na kasa NTA dake jihar
Kawara sun kama da wuta sakamakon wutar lantarki mai karfin
gaske da aka dawo da ita, da misalin karfi goma sha daya na dare.
Wannan na cikin wata sanarwar mai dauke da sa hannan Jami’in
hulda da Jama’a na gidan talabijin na jihar Kwara Hassan Adekunle.
A cewar sanarwar, ofishoshi Ashirin da takwas ne suka kone tare da
lalata muhimman takardu da dama.
Sanarwar ta kuma ce, ma’aikatar gidana telebijon din sun samu
nassarar kashe gobara ce da taimakon hukumar kashe gobara ta
jihar Kwara.
Ta cikin sanarwar, gwamnnar Jihar Abdulraman Abdulrazak ya
bukaci al’ummar jihar da su rungumi dabi’ar kashe makunnan wuta
don kiyaye aukuwar gobara a nan gaba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *