Hadarin tankar mai ya hallaka mutane 20
1 min read
Akalla mutane 20 suka kone kurmus sakamakon wata gobarar da ta tashi lokacin da tankar mai ta fashe akan hanyar Benin zuwa Sapele da ke Jihar Deltan Najeriya.
Rahotanni sun ce tankar man ta kama wuta ne lokacin da ta fada wani rami, abinda ya sa gobarar da ta tashi ta ritsa da matafiya da dama da ke cikin motocin su.
Shaidun gani da ido sun ce wutar da ta tashi ta kona akalla motoci 10, yayin da mutane da dama suka jikkata.
Rashin ingancin hanya na daga cikin abinda ke haifar da yawan hadura akan titunan Najeriya.