June 13, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Kwamitin Bincike zai baiwa Magu kwafin zarge-zarge

1 min read

Kwamitin shugaban kasa da ke binciken dakataccen shugaban hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta EFCC karkashin jagorancin tsohon shugaban kotun daukaka kara mai shari’a Ayo Salami, ya amince ya bai wa Ibrahim Magu kwafin bayanan zarge-zargen da a ke yi masa.
Tun farko dai kwamitin shugaban kasa da ke binciken kadarorin gwamnati ne ya zargi Ibrahim Magu ta cikin wani rahoto da ya mikawa ofishin attorney janar na kasa kuma ministan shari’a.
Sai dai rahotanni sun ce shugaban kwamitin Justice Ayo Salami ya shaidawa lauyan Ibrahim Magu Barista Wahab Shittu cewa za a basu kwafin rahoton amma da yarjejeniyar ba za a bari ‘yan jarida su gani ba.
Rahotanni sun ce a yau alhamis ake sa ran Ibrahim Magu zai fara kare kansa gaban kwamitin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *