June 13, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Majalisar dinkin Duniya tayi tofin ala tsine

1 min read

Majalisar dinkin duniya ta yi allawadai da kisan ‘yan kungiyar Boko Haram suka yi wa wasu ma’aikatan bayar da agaji guda biyar a jihar Borno, bayan kama su a Munguno cikin watan Yunin da ya gabata.
Wannan na cikin wata sanarwa da babban jami’in bayar da agaji na majalisar dinkin duniya a Najeriya Mr Edward Kallon ya fitar a jiya, yana mai nuna kaduwarsa da yadda ‘yan Boko Haram din suka hallaka ma’aikatan na su.
Edward Kallon ya mika sakon ta’aziyyarsa ga iyalan mamatan da sauran ‘yan uwa da abokan aikinsu.
A jiya laraba ne dai kungiyar Boko Haram ta fitar faifan bidiyon yadda suka kashe ma’aikatan agajin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *