Majalisar wakilan Najeriya za ta maka Akpabio a kotu
1 min read
Kakakin majalisar wakilan Najeriya Femi Gbajabiamila ya bukaci
Akawun majalisar ya gurfanar da ministan ma’aikatar Naija Delta
Godswill Akpabio a gaban kotu bisa zargin yi wa ‘yan majalisa kazafi.
Mr Gbajabiamila ya bayyana haka ne a shafinsa na Twitter ranar
Alhamis bayan wa’adin da ya bai wa Mr Akpabio na bayyana sunayen
‘yan majalisar da ya yi zargin suna karbar kwangila daga ma’aikatarsa
ya wuce.
“Da safiyar yau, na umarci Akawun Majalisar Wakilai ya dauko lauyoyi,
sanna ya bukace su da su shigar da karar da ta shafi aikata laifi kan
Ministan (Naija Delta). A lokaci guda, za mu duba yiwuwar umartar
layoyinmu su maka shi a kotu kan bata mana suna,” in ji Mr
Gbajabiamila.
A farkon mako ne Mr Akpabio ya yi zargin cewa ana bai wa ‘yan
majalisar dokokin tarayya kashi 60 cikin dari na kwangilolin da ake
bayarwa daga hukumar raya yankin Naija Delta, wato NDDC a takaice.
Lamarin ya bata ran ‘yan majalisar inda Mr Gbajabiamila ya ba shi
wa’adin.