April 15, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Rasuwar Isma’il Isah Funtuah babban rashi ne

1 min read

Wata kungiya mai suna Northern Media Forum, ta bayyana rasuwar Malam Isma’ila Isa Funtua a matsayin babban rashi a kasar nan da ketare, musamman ma a cikin harkokin aikin jarida.
Kafin rasuwarsa, Isma’ila Isa Funtua ya kasance jigo a cibiyar nazarin aikin jarida ta kasa-da-kasa shiyyar Najeriya, wanda ya yi yi fafuta wajen tabbatar da ‘yancin fadar albarkacin baki a kasar nan.
Wannan na cikin wata sanarwa da kungiyar ta fitar mai dauke da sa hannun shugabanta Dan Agbese, inda ya mika sakon ta’aziyyar kungiyar ga iyalan marigayin da kungiyar da shugaban kasa Muhammadu Buhari da kuma al’ummar jihar Katsina.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *