July 16, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Sai ministan Neja ya fadi wanda aka bawa kudi

2 min read

Yayin da wa’adin da majalisar dokokin Najeriya ta bai wa ministan ma’aikatar raya yankin Neja Delta kan fallasa ‘yan majalisar da yake zargi da cin gajiyar kaso mai tsoka na kwangilolin da hukumar NDDC ke bayarwa ke cika ranar Alhamis, ko me zai biyo baya?
Kakakin majalisar wakilan ƙasar Femi Gbajabiamila ne ya bai wa Godswill Akpabio umarnin bayan da ministan ya yi zargin cewa kashi 60 na kwangilolin hukumar an bai wa ‘yan majalisa ne ciki har da shugabanni biyu da suke jagorantar binciken baɗaƙala a hukumar.
Majalisar dai na gudanar da binciken almubazzaranci na fiye da naira biliyan 81, sama da dala 210,000 a hukumar.
An kafa hukumar ta raya yankin Neja Delta shekara 20 baya domin inganta rayuwar al’ummar yankin da ke da arzikin mai.
A ranar Litinin ne kuma bayan Shugaban hukumar ta NDDC, Daniel Pondei ya sha tambayoyi daga kwamitin majalisar aka ga ya kife kai kamar ya suma.
Daga nan aka garzaya da shi asibiti domin samun kulawa.
Ministan ma’aikatar raya Neja Delta yayin da ya bayyana gaban kwamitin a ranar Litinin, ya yi ikirari cewa “‘yan majalisar sune suka fi cin gajiyar kwangilolin da hukumar ta bayar.
Da aka tambaye shi ta yaya, ministan sai ya ce, “Yanzu na gama faɗin cewa muna da takardu da ke nuna cewa ‘yan majalisar dokoki ake ba wa akasarin kwangilolin na hukumar NDDC”.
Sai dai wannan iƙirarin ya fusata Kakakin majalisar wakilan, Mista Gbajabiamila inda ya ba da wa’adin sa’oi 48 ga ministan ya fitar da sunayen mutanen da suka ci gajiyar da kuma cikakken bayani kan kwangilolin da aka bai wa ‘yan majalisar ko kuma su fuskanci fushin doka domin dai ganin ya amsa umarnin majalisar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *