June 13, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Sau nawa aka taba soke Hawan Sallah a Kano?

1 min read

Sanarwar da gwamnatin jihar Kano ta fitar na soke bukukuwan
babbar sallah sakamakon annobar korona ba shakka ba za ta yi wa
jama’a da dama dadi ba.
Bukukuwan Sallah musamman hawan dawakai na daga cikin
abubuwan da ke kayatar da bikin sallah a kasar Hausa.
Annobar korona ita ce uzurin da gwamnati ta bayar na jingine bikin
Sallah a bana domin tabbatar da cewa ba a yi cunkoson da zai sake
yada cutar ba.
Ko a lokacin bikin karamar Sallah an hana bukukuwa da takaita
cudanyar mutane saboda wannan annobar. Sannan an gindiya wasu
sharuda don tabbatar da cewa mutane basu kamu ko sake yada
annobar korona ba.
Tabbas soke hawan babbar sallah zai zo wa wasu mutanen Kano ba
zata, kasancewar al’amura sun fara komawa kamar yadda aka saba,
sannan kuma ana ganin cewa wannan ne karon karon farko da
Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero zai yi cikakken hawa tun
bayan da ya zama sarkin Kano.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *