Yan bindiga sun hallaka sojojin Nigeria
1 min read
Adadin Sojin Najeriya da ‘yan bindiga suka hallaka a yankin Jibia na jihar Katsina ya karu zuwa mutum 23 sabanin 16 da wasu jaridun Najeriya suka wallafa a jiya Lahadi.
Kamfanin dillancin Labran Faransa AFP ya ruwaito wata majiya da ta nemi a sakaya sunanta na cewa an gano gwarwakin Sojin 23 yayinda har yanzu ake ci gaba da neman wasu da suka bace.
Wani Jami’in sa kai ya shaidawa AFP cewa adadin Sojin da suka mutu ka iya zarta alkaluman da ke da su a yanzu la’akari da yadda ake ci gaba da laluben sauran jami’an ko dai a raye ko kuma a mace.