June 13, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Bakin Bulo Network zata tallafawa marayu da yan gudun hijjira a yayin bikin sallah Babba.

1 min read

Kungiyar Bakin Bulo Network for Better Tomorrow ta bukaci al’umma dasu
tallafawa marayu dake unguwanni da naman layya domin rage musu radadin halin da suke ciki.

Shugaban kwamitin kula da marayu na kungiyar Hassan akibu hamza ne ya bayyana haka lokacin dake zantawa da yan jarida yan jarida a unguwar kuntau dake cikin karamar hukumar Gwale.

Akibu ya kuma ce marayu dake unguwanni suna cikin tsanin bukatar wadannan taimako kasancewar ana cikin yanayin annobar covid 19 wanda da yawa daga cikin al’umma na kwana cikin yunwa da fatara.
Ya kuma ce kungigar na neman sadakar fatah ko nama soyayye ko danye domin tallafawa ‘yan hudun hijira.

Domin bada wannan taimako za’a iya kiran wannan lamba kamar haka.
09036261002
+2348033477062
08149004687
Ko kuma a nemi P.r.o Bilal Nasidi Muazu

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *