July 16, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Mutane biyar ne suka kamu da corona a Kano a jiya Alhamis

1 min read

Hukumomi sun tabbatar da gano mutum biyar da cutar korona ta
kama ranar Alhamis a Kano, kwana guda bayan gano mutum 17 da
suka harbu.
Yawan mutanen da cutar ta shafa zuwa daren ranar ya kai 1,452
cewar hukumar dakile cutuka masu yaɗuwa ta kasar NCDC.
Alƙaluman ma’aikatar lafiya ta Kano sun nuna cewa yanzu haka
mutum 234 ne ke kwance suna ci gaba da jinya a cibiyoyin kula da
masu korona da ke jihar.
Jihar wadda a baya ta taɓa kai wa mataki na biyu cikin jerin jihohin
ƙasar 36 da kuma Abuja, yanzu ta koma mataki na bakwai, saboda
raguwar masu kamuwa da cutar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *