June 23, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Nigeri: Mutane 20 suka sake kamuwa da corona cikin sa’a biyu.

1 min read

Alƙaluman da hukumar dakile cutuka masu yaɗuwa ta fitar sun nuna
cewa cutar korona ta sake kashe mutum 20 a faɗin Najeriya. Da
wannan, cutar ta yi ajalin mutum 833 ke nan a ƙasar.
A Legas inda cutar ta fi ƙamari, mutum 203 ne annobar ta sake
harba, yayin da aka samu ƙarin mutum 79 a Abuja, babban birnin
tarayya.
NCDC ta kuma nuna cewa masu korona 246 sun warke daga cutar,
har ma an sallame su ranar Alhamis don komawa gida cikin iyalansu.
Ƙididdiga ta nuna masu korona 22,887 ne ke kwance suna jinya a
cibiyoyin kwantar da masu cutar na faɗin Najeriya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *