July 16, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Rundunar yan sandan kano ta kama ‘yan bindiga da wasu tarin makamai.

1 min read

Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta ce jami’anta sun kama bindigogi
da dama, da wasu mutane waÉ—ada ake zargin yan fashi ne ke amfani
da su wajen aiwatar da ayyukansu.
Kwamishinan rundunar a Kano Habu Sani ne ya bayyana hakan yayin
da yake jagorantar holin mutum 392 da rundunar ta ce ta kama bisa
zargin aikata laifuka daban-daban.
Bindigogin sun hadar da kirar Ak47 guda uku, da wasu samfurin
Pistol guda biyu, da na gargajiya wato harbi ka ruga guda uku, baya
ga harsasai 1,087.
Ta ce ana zargin mutanen na amfani da makaman ne wajen aikata
laifukan fashi da makami, garkuwa da mutane, zamba cikin aminci,
da kuma ayyukan daba.
Rundunar ta kuma ce sun kama mutanen ne daga ranar 15 ga watan
Mayu, zuwa 22 ga watan Yulin da muke ciki.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *