July 16, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

‘Yan Majalisar Sarki 5 Sun Yi Murabus

2 min read

Masarautar Shinkafi dake Jihar
Zamfara a arewacin Najeriya, ta nada Femi Fani
kayode, tsohon Ministan Sufurin Jirgin Saman Najeriya
a matsayin sarautar Sadaukin Shinkafi, lamarin da bai
yiwa al’ummar Shinkafi dadi ba.
‘Yan majalisar Sarkin su biyar sun yi murabus don
nuna adawa da nadin da Sarki Muhammad Makwashe
yayi.
Dr. Tijjani Salihu daya daga cikin ‘yan majalisar sarki,
kuma malami a jami’ar Usman Dan Fodio Sokoto, ya
shaidawa wakilin muryar Amurka cewa, yayi murabus
daga mukaminsa na “Uban Marayun Shinkafi” saboda a
cewar sa an baiwa makiyin arewacin Najeriya sarauta,
kuma mai yawan sukar sarkin Musulmi, kuma hakan
abin bakin ciki ne.
Shi ma Alhaji Sulaiman Shu’aibu, wanda yayi murabus
daga mukamin sa na “sarkin Shannun Shinkafi”, ya
bayyana wa wakilin muryar Amurka dalilin sa na ajiye
wannan mukami, cewar bai amince da aka baiwa Femi
Fani kayode sarautar Saukin Shinkafi ba, saboda ya
dade yana sukar arewa da shugabanninta.
Ya kara da cewa sarautar Sadauki, sarauta ce mai
daraja, wanda duk wanda yake da sarautar zai iya
sadaukar da rayuwar sa da dukiyar sa ga al’ummar
yankin, da addinin su da al’adun su da zamantakewar
su, da kuma kare mutunci da muradun wadannan
al’umma.
Mai bada shawara na musamman ga gwamnan jihar
Zamfara, Alhaji Zailani Baffa ya shaidawa wakilin
muryar Amurka cewa, gwamnati ba ita take zabar duk
wata sarauta ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *