September 22, 2023

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

A Ranar Juma’a za’a gudanar da bikin Sallah Babba a Nigeria

1 min read

Mai alfarma sarkin musulmi Alhaji Sa’ad Abubakar na uku ya bayyana ranar juma’a talatin da daya ga wannan wata na Yuli a matsayin ranar babbar sallah.

Hakan na cikin wata sanarwa ce mai dauke da sa hannun shugaban kwamitin ba da shawara kan harkokin addini ga sarkin musulmi, farfesa Sambo Junaidu.

Haka zalika sanarwar ta kuma bayyana cewa, mai alfarma sarkin musulmin ya bukaci dukkannin hakimai da dagatai da ke masarautar Sokoto da su yi sallarsu a masallatan juma’a, saboda kare kai daga cutar corona.

Sanarwar ta kuma bukaci sauran al’ummar musulmi a ko ina a fadin kasar nan da su gudanar da sallarsu ta Idi a masallatan juma’a, don dakile yaduwar cutar ta covid-19.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *