June 13, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Daukar wasanni da muhimmanci zai samarwa matasa kudi-Yarima Lamido Abubakar Bayero

2 min read

Yariman Kano Alhaji Lamido Abubakar Bayero ya yi kira ga matasa da su rinka bawa harkokin wasanni muhimmanci ta hanyar da zata taimaka musu wajen samun kudi tare da zama masu dogaro da kai.

Yariman na Kano ya yi wannan kiran ne lokacin da ya kai ziyarar taya murna ga sabon mataki na musamman ga gwamnan jihar Kano kan al’amuran wasanni Alhaji Ibrahim Mu’azzam Madaki.

 Ya bayyana cewa nadin Ibrahim Mu’azzam an ajiye kwarya a gurbinta duba da irin gudummawar da yake bayarwa a bangaren wasanni da ci gaban matasa duba da yadda yake gayyato turawa suna daukar ‘yan wasa a jihar Kano.

Yariman na Kano ya kuma bukaci sabon mataimakin na gwamna ya yi amfani da kwarewar sa wajen kawo ci gaba mai dorewa a bangaren wasanni da ci gaban matasa a jihar Kano.

 Da yake maida jawabi Alhaji Ibrahim Mu’azzam Madaki ya godewa Yariman Kano kan ziyarar da ya kawo masa, inda ya bayyana cewa masu rike da sarautar gargajiya suna da rawar da zasu taka don kawo ci gaba a bangaren wasanni ta hanyar wayar da kan iyaye yadda zasu bar ‘ya’yansu su shiga harkar ba tare da sun daina karatu ko tarbiyyar su ta lalace ba.

Ya kara da cewa gwamnatij jihar Kano zata yi aiki kafada da kafada da masu rike da mukaman gargajiya domin samar da ci gaban da ake bukata a harkokin wasanni.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *