Dogara ya gana da Buhari bayan komawarsa APC
1 min read
Tsohon Kakakin Majalisar Wakilan Najeriya, Yakubu
Dogara ya koma Jam’iyyar APC mai mulki, yayin da ya
gana shugaba Muhammadu Buhari a fadarsa da ke birnin
Abuja. Gwamnan Yobe kuma Shugaban Riko na Kwamitin Amintattun
Jam’iyyar APC, Mai Mala Buni ya tabbatar da sauyin shekar Dogara a
yayin zantawa da manema labarai a birnn Abuja.
Buni ya ce, kar ‘yan Najeriya su yi mamakin sauyin shekar saboda
tsohon shugaban Majalisar Wakilan, mamba ne na jam’iyyar APC,
kuma a yanzu an magance dalilin da ya sa ya fice daga cikinta a can
baya.