June 13, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Dole Buhari ya sauka daga kan mulki saboda karancin tsaro

1 min read

Babbar Jam’iyyar adawa a Najeriya ta PDP ta bukaci
shugaban kasar Muhammadu Buhari da ya sauka daga
mukaminsa saboda yawan kashe-kashen da ake ci gaba
da samu a kasar da kuma cin hanci da rashawar da suka
dabaibaye harkokin gwamnatinsa. Jam’iyyar wadda ta bayyana haka a taron manema labarai ta ce,
gwamnatin Buhari ta rude ta kuma rasa abin da za ta saka a gaba
wajen yaki da Kungiyar Boko Haram da masu garkuwa da mutane da
kuma ‘yan bindigar da ke kashe jama’a ba ji ba gani.
Shugaban Jam’iyyar Uche Secondus ya ce matsayin Majalisar
Dattawa cewar shugabannin rundunonin sojin kasar su sauka daga
mukamansu saboda gazawa wajen kare lafiyar jama’a, ya nuna
cewar bangaren zartarwa ba ya aikin da ya rataya a kansa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *