June 13, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Hukumar Alhazan Nigeria zata fara karbar kudin aikin haji.

2 min read

Shugaban Hukumar Zikirullahi
Olakunle Hassan ne ya bayyana haka a wani taron
manema labarai a Abuja.
Wakiliyar Sashin Hausa Medina Dauda ta halarci taron,
kuma ta aiko mana cewa, Shugaban Hukumar Alhazai
Barista Zikirullah Olakunle Hassan ya ce hukumar za ta
fara karbar Kudin maniyyata aikin Hajjin shekarar 2021
daga ranar 9 ga watan Satumba.
Ahaji Hassan ya kara da cewa hukumar, za ta bude
wani sabon shafi na yanar gizo domin saukaka wa
maniyyata rajista.
A lokacin da yake karin haske akan batun ko wasu
maniyyata da ba su samu tafiya aikin hajjin bana ba za
su kar6i kudadensu, Shugaban Hukumar Alhazan ya
shawarci maniyyata aikin hajjin na badi da su fara
tanadin kudadensu tun yanzu domin yin adashin gata a
asusun hukumar.
Wani abinda ya dauki hankali shi ne yadda cutar
coronavirus ta sa kasar Saudi Arabiyya ta soke aikin
hajjin bana, sannan kuma ta yi karin kudaden haraji a
kasar ta Saudiyya, to ko wanan kari zai shafi kudaden
da Alhazai za su biya ?
Sai Kwamishina a Hukumar Alhazan Nura Ahmed
Yakasai ya ce, “Abu guda daya da ya tabbata shi ne
kasar Saudiyya ta yi kari ne akan haraji kawai, bayan
shi abubuwa kaman makwanci da motocin sufuri ba a
tabbatar da karin ba tukuna, tunda kowace shekara
irin wadannan suna canjawa saboda haka burin
hukumar shine a samu sauki saboda duk maniyyaci
daga Najeriya ya samu halartar aikin Hajji.”
Yanzu dai abin jira a gani shi ne irin nasarar da za a
samu wajen gano maganin cutar coronavrus ko na
rigakafinta saboda maniyyata su samu damar yin aikin
hajjin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *