April 23, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Kano-Matashi ya kashe kansa bayan da ya sami labarin cewa an kawo kudin auren budurwarsa.

1 min read

Wannan m matashi mai suna Ashir Musa Sani ‘dan shekara 24ya hallaka kansa ta hanyar cakawa kansa wuka, a unguwar Dan Rimi dake karamar hukumar Ungogo.

Mahaifin matashin mai suna Musa Sani ya ce ana zargin ‘dan nasa ya hallaka kansa ne bayan da ya samu labarin cewar an kawo kudin auren budurwar da yake so.

Kakakin rundunar ‘yan sanda ta jihar Kano, DSP. Abdullahi Haruna Kiyawa ya tabbatar da faruwar al’amarin, inda ya ce, matashin ya rasa ransa ne bayan da ‘yan uwansa suka kai shi asibiti sanadiyyar galabaitar da yayi bayan da ya cakawa kansa wuka.

Yanzu haka dai, tuni aka yi jana’izar sa, kamar yadda addinin musulunci ya tanadar.
Wasu makusantan mamacin mai suna dauda ya ce matashin mutum ne mai hakuri da juriya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *