July 12, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Kano-za’a yiwa masarautu kwaskwarima.

1 min read

A mako mai zuwa ne ake sa ran majalisar dokokin jihar Kano za ta
dauki matsaya kan bukatar da gwamnan jihar Abdullahi Umar
Ganduje ya gabatar mata na yin gyara ga dokar Masarautun Kano ta
2019.
A farkon makon ne gwamnan jihar Abdullahi Umar Ganduje ya
gabatar wa Majalisar Dokokin jihar bukatar yi wa dokar Masarautun
jihar ta 2019 kwaskwarima, don ganin an kara Sarkin Dawaki Babba a
cikin masu zaben Sarkin Kanon.
A ranar Larabar da ta gabata ne shugaban Majalisar Dokokin jihar
Abdul’aziz Garba Gafasa ya karanta takardar a yayin zaman
majalisar.
Matakin na zuwa ne a yayin da Masarautar Kano take jiran amsar
gwamnati a hukumance kan bukatar nada Alhaji Aminu Babba
Danagundi a matsayin Sarkin Dawaki Babba da kuma Alhaji Sanusi
Ado Bayero a matsayin Wamban Kano
Marigayi Sarkin Ado Bayero ne ya sauke Aminu Babba daga sarauta,
yayin da tsohon Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II ya sauke Lamido
Ado Bayero.
Aminu Babba, ya kalubalanci sauke shi da a kotu, amma Kotun Ƙoli
ta tabbar da sauke shi bayan shekara 17 ana shari’a.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *