July 18, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Labari da dumi-duminsa An sanya dokar hana fita yanzu-yanzu

1 min read

Gwamnan jihar Kaduna Nasir El-Rufai ya saka dokar hana fita ta
tsawon sa’a 24 a ƙananan hukumomin Jema’a da kuma Kaura.
Tuni dama an saka irin wannan dokar a ƙananan hukumomin Kauru da
kuma Zangon Kataf domin daƙile rikicin da ke yankin.
A daren Juma’a ne gwamnan ya bayyana hakan bayan wani hari da ‘yan
bindiga suka kai a wasu yankuna na Jema’a da kuma Maraban Kagoro
duk a ƙaramar hukumar ƙaura ta jihar Kaduna.
A saƙon da gwamnan ya wallafa a Twitter, ya kuma bayyana cewa tun a
2017 aka ƙara kai dumbin jami’an tsaro kudancin Kaduna bayan da aka
gina wani sansanin sojoji a Kafanchan.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *