April 14, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Nada Ibrahim Mu’azzam zai bunkasa harkokin wasanni a Jihar Kano.

2 min read

Wasu kungiyoyin kwallon kafa a jihar Kano sun yabawa gwamnan Kano Dakta Abdullahi Umar bisa nada kwararren masani a harkokin wasanni Ibrahim Mu’azzam Madaki a matsayin mai taimaka masa na musamman kan al’amuran wasanni.

Cikin ziyarar taya murna da suka kawo ofishin a lokuta daban-daban kungiyoyin sun bayyana cewa wannan nadi da aka yi an ajiye kwarya a gurbinta, duba da irin kwarewa da sabon SSA din ke da ita a fannin gudanar da harkokin wasanni tare da irin ci gaba da ya kawo a kungiyoyin kwallon kafa da ya jagoranta a ciki da wajen jihar Kano.

Kungiyoyin sun bukaci Ibrahim Mu’azzam Madaki da yayi amfani da kwarewarsa wajen kawo ci gaba mai dorewa a jihar Kano ta fannin wasanni da ci gaban matasa.

Kungiyoyin da suka kawo ziyarar sun hada da Ganduje Babies, Kano traveling FC, Star Light FC, Jaen United, Dabo Babies, Peace United, Kano Lions FC da kuma wasu kungiyoyin da dama.

Idan za’a iya tunawa a ranar 9 ga watan Yunin shekarar 2020 gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya nada Ibrahim Mu’azzam Madaki a matsayin mai taimaka masa na musamman kan harkokin wasanni.

Sabon SSA din ya shafe sama da shekaru 25 yana gudanar da harkokin wasanni a ciki da wajen jihar Kano, inda ya tallafawa ‘yan wasa da dama wajen samun damar fita kasashen waje domin buga wasa a manyan kungiyoyi.

Haka kuma yana daya daga cikin shugabannin hukumar kula da wasannin gargajiya ta kasa.

Har zuwa lokacin wannan nadin shine shugaban kungiyar Star Light Academy, kungiyar tana buga gasar Amateur 2 a jihar Kano.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *