June 13, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Rabiu kwankwaso ya ce ya san yadda za’a daina handime kudin Neja Delta

1 min read

Wani fitaccen ɗan siyasa a Najeriya ya yi iƙirarin cewa za a ci gaba
da sace dukiyar raya yankin Neja Delta da ma sauran ma’aikatun
ƙasar, matuƙar shugabanci ba zai zura ido kan kuɗaɗen da ake
fitarwa ba.
Matuƙar ba za a yi ƙoƙarin tabbatar da ganin kowanne kobo an yi
amfani da shi a inda ya dace ba, ba shakka za a ci gaba da samun
matsaloli wajen tsare amanar dukiyar al’umma, in ji Rabi’u Musa
Kwankwaso.
Tsohon gwamnan Kano wanda ya taɓa aiki a matsayin wakili cikin
kwamitin gudanarwar hukumar raya yankin Neja Delta (NDDC) kafin
ya yi murabus a 2010, na wannan jawabi ne ta cikin shirin Ra’ayi
Riga na BBC Hausa.
Jigon ɗan adawar ya nuna cewa mayar da hukumar ƙarƙashin ofishin
shugaban ƙasa, ba lallai ne ya yi wani tasiri ba, don kuwa a baya ma
an taɓa yin hakan ba tare da samun sauyin a-zo-a-gani ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *