July 16, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Ambaliyar ruwa ta kashe mata da ‘ya’yanta huɗu.

1 min read

Wata mata mai ciki tare da ‘ya’yanta huɗu na cikin waɗanda suka rasa rayukansu sakamakon ambaliyar ruwa a yankin Gwagwalada da ke Abuja, babban Birnin Tarayyar Najeriya. Matar ‘yar shekara 27 mai suna Habibat Hameed ta rasu tare da yaranta; Latifat da Rahamat da Abdulateef da kuma Rabiu, a cewar rahoton jaridar Daily Trust . Hotuna da bidiyo da aka wallafa a Twitter sun nuna yadda ruwa ya shafe gidaje da hanyoyin mota.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *