July 16, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

An kama wasu manyan mutane biyu sunyi lalata da wata ‘yar shekara 15 a cibiyar killace masu corona.

1 min read

An zargi wani matashi da yin lalata da wata yarinya ‘yar shekara 14 a
cikin wata cibiyar killace masu cutar korona a Delhi, babban birnin
Indiya.
Wanda ake zargin ɗan shekara 19 da kuma wani mutum da ake zargin
ya naɗi abin da ya faru a bidiyo, duka an kama su, a cewar ‘yan sanda
ranar Alhamis.
Dukkanin mutum ukun sun kamu da cutar ta korona ne amma ba ta
kwantar da su ba kuma suna killace ne a cibyar da ake ganin ta fi
kowacce girma a Indiya – mai cin gado 10,000.
Tun ranar 15 ga watan Yuli lamarin ya faru amma sai yanzu labarin ya
fito.
A makon da ya gabata, an yi zargin yin lalata da wata mata a cikin wata
cibiyar killacewa da ke Mumbai sannan an kama wani mutum a Jihar
Bihar bayan an samu rahoton cewa an yi wa wata ƙaramar yarinya
fyaɗe a wata cibiyar ta killace masu korona.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *