July 18, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

An kashe manoma 20 a wani kazamin hari.

1 min read

‘Yan bindiga sun kashe a ƙalla mutum 20 lokacin da suke koma wa
gonakinsu karon farko cikin shekaru cewar wasu rahotanni daga
yankin Darfur na ƙasar Sudan.
An kuma ce ƙarin mutum ashirin sun ji raunuka a harin da aka kai
yankin Aboudos, mai nisan kilomita 90 kudu da Nyala, babban birnin
lardin Darfur ta Kudu,
Yankin Darfur na fama da rikici kimanin tsawon shekara ashirin.
Faɗa tsakanin ‘yan tawaye da dakaru masu biyayya ga tsohon
shugaba Omar Hassan al-Bashir ya raba miliyoyin mutane da
muhallansu, an kuma kashe ƙarin wasu dubban ɗaruruwa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *