An soke hawan Sallah a Jihar Katsina
1 min read
Masarautar Katsina da ke arewa maso yammacin Najeriya ta dakatar da
hawan Babbar Sallah sakamakon matsalar tsaro da kuma cutar korona.
Cikin wata sanarwa da Sakataren Masarautar kuma Sallaman Katsina
ya fitar ranar Laraba, Alhaji Bello M. IFO ya ce Mai Martaba Sarkin
Katsina, Alhaji Dr. Abdulmumini Kabir Usman da ‘yan majalisarsa ne
suka yanke shawarar dakatar da hawan Sallar.
“Bisa ga tashe-tashen hankalin da ake samu na ‘yan ta’adda wanda
yake jawo sanadiyyar rasa rayuka da kuma dukiyoyi da iftila’i na cutar
Covid-19 (korona)…an umarce ni na faɗa muku ba za a samu damar
yin hawan Sallah Babba ba,” in ji sanarwar.
“Don haka za mu ci gaba da yin addu’o’i na samun zaman lafiya.”
Ita ma gwamnatin Jihar Kano ƙarƙashin jagorancin Gwamna Abdullahi
Umar Ganduje ta dakatar da bikin Sallah a jihar.