June 23, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Ana Ci Gaba Da Muhawara Kan Badakalar Kudaden Yankin Niger Delta

2 min read

A Najeriya ana ci gaba da cece-
ku-ce akan batun binciken badakalar biliyoyin Naira da
Majalisar Dokoki ta gano a hukumar da ke kula da
yankin Niger Delta, abinda ke nuni da cewa dara ce za
ta ci gida domin ‘yan jam’iyyar APC ne ke barazanar
gurfanar da junansu a gaban kotu.
Batu na baya bayan nan shi ne wanda kakakin
Majalisar Wakilai Femi Gbajabiamilla ya bada umurnin
shigar da kara akan Ministan Ma’aikatar Niger Delta
Godswill Akpabio muddun ya gaza kawo hujja akan
ikirarin da yayi cewa ‘yan Majalisa ne suke karbe
kwangilolin Hukumar ta NDDC.
To sai dai kwararru a fannin sha’ria da ma wasu ‘yan
jam’iyyar APC sun bayyana ra’ayinsu akan tanadin da
kundin tsarin mulkin kasa ya yi akan irin wannan
yanayi da jam’iyyar ta tsinci kanta a ciki, inda
kwararre a fannin kundin tsarin mulkin kasa Barista
Mainasara Ibrahim Umar ya ce sashi na 36 na kundin
tsarin mulki ya ba kowa dama na neman hakkinsa a
kotu idan an yi masa ba daidai ba, ko an muzguna
masa akan wani abu da ba a tabbatar ba.
Shi ma Barista Nura Danbatta ya kara jadadda cewa
majalisa ta na da hurumin neman hakkinta musamman
ma wanda ya jibanci bata masu suna, amma tunda
Minista Godswill Akpabio ya yi nadama ya ce ba haka
ya ke nufi ba, to ‘yan majalisa ya kamata su janye
maganar su rabu da Akpabio, su fuskanci aikinsu.
Amma daya daga cikin ‘yan jam’iyyar kuma shugaban
tsare-tsare na gundumar Gwange a Jihar Yobe, Saleh
Bakoro Sabon Fegi, ya na ganin shugabannin Majalisar
su yi hattara wajan kalubalantar junansu a fili, saboda
tamkar suna burma wa cikinsu wuka ne.
Saleh ya ce ya kamata su sulhunta matsalolinsu a cikin
gida ba lallai dole sai mutane sun ji abinda ke
tsakaninsu ba, duk da haka idan ta tabbata cewa an
muzguna wa mutum, to fa ya na iya neman hakkinsa a
gaban kuliya.
Ita kuwa Majalisar Dattawa umurni ta ba ma’aikatan
hukumar Niger Delta akan su maida wa asusun
gwamnati Naira biliyan 1.336 da suka rarraba wa
kansu, akan dalilin kalubalantar cutar coronavirus.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *