Kotun tafi da gidanka zata fara yan kewa mutanan da basa amfani da safar hanci a Kano.
1 min read
A yayin wani taron manema lavarai a yau Ganduje jihar Kano ta ce ta fito da kotun tafi da gidanka da zata rika hukunta wadanda basa bin dokar Sanya Safar baki da hanci wacce Sanya tan zai Zama kariya daga yaduwar Cutar Corona.
Gwamna Dr Abdullahi Umar Ganduje ya bayyana hakan ne a yau lokacin da yake sake kaddamar da rarraba safar Baki da hanci a fadar gwamnatin Kano
Gwamna Dr Ganduje ya Kara da cewa zasu hada kai da jamian tsaro da sauran masu ruwa da tsaki don tabbatar da mutane na karya dokar.
Da yake jawabi shugaban kwamitin karta kwana kan cutar Corona kuma mataimakin gwamnan Kano Nasir Yusif Gawuna Kira yayi kungiyoyin sufuri da tabbatar da Sanya safar lokacin gudanar da aikin su da fasinjojin su.
Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero ya ja hankalin alummar jihar nan da suyi amfani da dokar da gwamnatin ta kafa na hakura da bukukuwan Sallah da yawace yawacen Sallah don Kare Kai daga yaduwar Cutar Corona.