June 13, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Likitoci sama da dubu goma ne suka kamu da corona

1 min read

Ma’aikatan lafiya fiye da 10,000 ne suka kamu da cutar korona a
Nahiyar Afrika tun bayan ɓullar cutar, a cewar Dr Ambrose Talisuna na
Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO).
Dr Talisuna mai bayar da shawara ne a ofishin hukumar a Afrika kuma
ya ce yanayin “mai tsoratarwa ne sosai”.
Ya yi kira ga ƙungiyoyin agaji da su taimaka wurin tabbatar da cewa an
faɗakar da ma’aikatan lafiyar sannan a kare su.
Ya ƙara da cewa WHO “ta wallafa tsarin yadda za a kare kai daga cutar”
da kuma bai wa ma’aikatan lafiya 50,000 horo.
Dr Talisuna ya nanata cewa ɗaiɗaikun ƙasashe na da rawar da za su
taka don ganin an kiyaye likitocin ta hanyar samar musu da kayan
kariya wato PPE da kuma rage musu tarin ayyuka.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *