Mahajjata sun killace kansu kafin fara aikin Hajji
1 min read
Mahajjatan da suka isa garin Makkah sun fara killace kansu kafin su
ɗunguma zuwa Mina ranar Laraba 8 ga watan Zul Hijjah, wadda ake
kira Tarwiya.
Tarwiyah tafiyar kilomita kusan bakwai ce daga garin Makkah zuwa
Mina a matsayin wani ɓangare na aikin Hajji.
Mahajjatan sun fito ne daga garuruwan Madinah da Riyadh da Abha da
Tabuk da kuma Jazan, a cewar rahoton kamfanin dillancin labarai na
SPA wanda kuma Saudi Gazette ta ruwaito.
Mataimakin Ministan Hajji da Umara, Dr. Abdul Fattah Mashat ya
jaddada “haɗin kan kai da aiki tare” da ake yi tsakanin ma’aikatar
harkokin cikin gida da ta lafiya da kuma jami’an tsaro.
Da yake magana da SPA, Dr. Abdul Fattah ya ƙara da cewa mahajjata
‘yan ƙasashen waje 160 ne za su gudanar da aikin Hajjin na bana.
Ya ce an zaɓi mahajjatan ne ta hanyar cike fom ta intanet, yana mai
ƙaryata rahotannin cewa an yi wa wasu alfarma. Ya ƙara da cewa
waɗanda suka cika sharuɗɗan lafiya ne kaɗai aka bai wa damar yin
aikin.