July 16, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Manchester United ta samu tikitin kofin Zakarun Turai

1 min read

Kungiyar Kwallon kafa ta Manchester United, ta kai bantan ta da kyar a kokarin neman tikitin zuwa gasar kofin Zakarun Turai na Champions league , bayan samun Nasara a wasanta da abokiyar burminta ta Leicester City.

Wasan wanda shi ne na karshe wato wasa na 38 a gasar kakar wasanni ta bana,2019/2020 , Manchester ta samu nasarar da ci biyu da nema a filin wasa na Kingpower Stadium , dake birnin na Leicester.

Bayan tafiya hutun rabin lokaci a zagaye na biyu, dan wasa Bruno Fernandez ya zura Kwallo a minti na 71 da bugun daga kai sai mai tsaron gida bayan da dan wasa Martial ya samo bugun.

Ana gab da za a tashi wasa a minti na 90 mai tsaron gida na Leicester City , Kasper Schemiechel ya yi kuskuren turawa dan wasan gaba na tawagar Manchester Jesse Lingard Kwallo, wanda take ya yi amfani da damar wajen zura Kwallo ta biyu ta tawagar tashi , kana ya tabbatar da kasancewar su a gurbi na hudu kana na karshe na kungiyoyin da zasu wakilci kasar a gasar Champions league na shekarar gaba, bayan samun maki 66.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *