Ministan sadarwa Pantami yayi fatali da karin kudin lasisi da rijista
2 min read
Ministan Sadarwa a Najeriya, Isa Ali Pantami ya yi watsi da sabon
tsarin cazar kuɗin neman lasisi ko rajista a kan kamfanonin kai saƙo da
Hukumar Aika Saƙonni ta Najeriya (NiPOST) ta fito da shi.
Mista Pantami ya bayyana hakan ne ranar Asabar a wani saƙon Twitter
da ya wallafa, yana mai cewa hukumar ba ta samu sahalewarsa ba
domin aiwatar sabon tsarin.
“Mun samu labarin wani ƙari game da kuɗin rajista, wanda ba ya cikin
dokokin da na sahale muku,” in ji Pantami.
“An shaida wa shugabanku a jiya cewa su dakatar da shirin sannan su
aiko da rahoto ga ma’aikatarmu zuwa ranar Litinin. Ina yi muku fatan
alheri.”
Daga cikin sabon tsarin da Nigerian Postal Service (NIPOST) ta fito da
shi, duk kamfanin da ke zirga-zirgar isar da saƙo a faɗin Najeriya zai
biya naira miliyan 10 idan zai yi rajista sannan duk shekara ya biya
miliyan huɗu.
Kamfanin da ke aiki a yankuna kuma zai biya miliyan biyar ne sannan
ya biya biya miliyan biyu duk shekara.
Haka ma kamfanonin da ke aiki a iya cikin jihohi za su biya miliyan biyu
don yin rajista, waɗanda kuma ke zirga-zirga a cikin birane za su biya
miliyan ɗaya na rajista da kuma N400,000 duk shekara.
Wannan ya haɗa da duk wani kamfani da ke aikin karɓa da isar da
saƙonni a Najeriya.