June 13, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Sojojin Nigeria sun gano sansanin yan bindiga a Zamfara

1 min read

Wasu hare-hare da dakarun sojan sama na Najeriya suka kai ya yi
sanadiyyar tarwatsa wani sansanin ‘yan fashi a Jihar Zamfara da ke
arewa maso yammacin ƙasar, a cewar hedikwatar tsaron Najeriya.
Sanarwar da hedikwatar tsaron ta wallafa a yau Asabar ta ce dakarun
rundunar musamman ta Operation Hadarin Daji sun kai harin ne a Dajin
Doumborou ranar Juma’a bayan sun samu wasu bayanan sirri.
Kazalika ta wallafa wani bidiyo a shafinta na Twitter, inda ta ce na harin
ne.
“Harin da rundunar Operation Hadarin Daji ta kai ya haifar da
kyakkyawan sakamako ta hanyar tarwatsa sabon sansanin ‘yan fashi
ƙarƙashin jagorancin ‘Dangote,'” in ji sanarwar.
Sai dai rundunar ba ta bayyana adadin waɗanda ta kashe ba ko kuma
suka ji rauni daga cikin ‘yan fashin, haka ma ba ta bayyana ko an samu
rasa rai daga ɓangaren nata dakarun ba.
Wannan hari na ɗaya daga cikin waɗanda rundunar ta sha ikirarin kai
wa ‘yan fashin, waɗanda suka kashe mutane da dama tare da hana
mutanen yankin jihohin Katsina da Zamfara da Sokoto.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *