June 13, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Yan Najeriya na kan hanyar komawa gida daga Faransa

1 min read

Wani rukunin ‘yan Najeriya daga ƙasar Faransa na shirin komawa gida
a yau Lahadi.
Hukumar ‘Yan Najeriya Mazauna Ƙasashen Waje (NIDCOM) ta ce
jirginsu zai bar filin jirgi na Charles de Gaulle da ke birnin Paris da
ƙarfe 10:35 na safiya agogon Najeriya – nan da minti 36 kenan.
‘Yan Najeriyar da suka fito daga ƙasashen Turai daban-daban, za su
sauka a filin jirgin sama na Nnamdi Azikiwe da ke Abuja babban birnin
ƙasar.
Dubban ‘yan Najeriya ne suka koma gida daga ƙasashen waje
sakamakon maƙalewa da suka yi a ƙasashen da ba nasu ba saboda
dokokin kulle da har yanzu ke aiki a wasu biranen duniya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *