June 13, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Ƴan Kwankwasiyya sun gurfanar da Gwamna Ganduje a gaban kuliya

1 min read

Reshen Ɗariƙar Kwankwasiyya na jihar Kano ya maka gwamnatin
jihar a kotu don hana ta ciyo bashin €684,100.100.00 daga China
Development Bank don samar kuɗaɗen gudanar da aikin titin jirgin
ƙasa a jihar.
Kwankwasiyya ta kuma rubuta ƙorfi a kan gwamnatin jihar Kano da
Majalisar Dokokin Jihar Kano zuwa Shugaban Majalisar Dattijai ta
Najeriya, Ma’aikatar Kuɗi ta Ƙasa, Ofishin Bada Bashi na Ƙasa,
Ofishin Jakadancin China da Chinese Development Bank, tana mai
cewa an saɓa ƙa’ida a buƙatar ciyo bashin, kamar yadda jaridar
Intanet, Daily Nigerian ta rawaito.
A wata sanarwa da Aminu Abdussalam, ɗan takarar mataimakin
gwamna a jam’iyyar PDP a zaɓen gwamna na 2019 ya sanya wa
hannu, Kwankwasiyya ta yi kira ga kowa da kowa da ya ƙalubalanci
wannan shiri na ciyo bashi, saboda a cewarta kuɗin zai ƙare ne “a
aljihun babbar rigar Gwamnan Kano”.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *