June 12, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Afrika Ta Kudu: An kama fursunoni 68 da suka tsere daga gidan yari

1 min read

Jami’an tsaro sun kama duka ‘yan fursunan da suka tsere daga
gidan yari a Afrika Ta Kudu a ranar Juma’a.
An dai yabi gandirebobin gidan yarin sakamakon shafe kusan
kwanaki biyu suna bin sawun ‘yan fursunan da suka tsere.
Rikicin da ya sa suka tsere ya faru ne bayan fursunonin sun sha
ƙarfin gandirebobin da ke gidan yari na Malmesbury yayin wani
atisaye.
Hakan ya sa fursunonin suka rufe gandirebobin cikin ɗaki kafin suka
saki ‘yan uwansu da ke tsare sa’annan suka haura ta katanga kuma
suka gudu, in ji hukumomi.
Rahotannin da aka bayar a baya dai sun ce fursunonin sun tsere ne
yayin da ake kan hanyar kai su wurin shari’a.
Hukumar gyara ɗabi’u ta Afrika Ta Kudu a baya dai ta ce fursunoni
68 ne suka tsere, sai dai daga baya ma’aikatar shari’a ta ƙasar ta
bayyana cewa jumullar mutum 68 ne suka gudu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *