June 13, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Akwai yuhuwar bude Makarantu a kasar nan

2 min read

A yau ne ake saran cewa gwamnatin tarayya da na jihohi za su gana wajen sake yin nazari kan bin dokokin da aka sanya musu, domin yanke shawarar ranar da za’a bude makarantu a kasar nan.
A dai kwanakin baya ne ma’aikatar ilimi ta kasa ta aikewa shugabanin makarantu kudin bayanai mai dauke da shafuka 52 na bin dokokin da aka shifida musu da zai baiwa dalibai na karshe rubuta jarrabawar a makaratu duk da annobar Corona da ake fama da shi a kasar nan.
Babban sakatare a ma’aikatar ilimi Mr. Sonny Echono ya sanar da hakan cewa, da zarar an kammala ganawar ne ake saran cewar za’a sanar da ranar da za’a bude makarantu a Najeriya.
Ganawar wacce za’a yi ta kafar Internet tare da hukumomin ma’aikatar ilimi da kwamishinonin ilimi na jihohin kasar nan 36 har da na babban birnin tarayya Abuja.
Mr Sonny Echono ya kara da cewar daga cikin wadanda ake sa ran za su shiga ganawar akwai, hukumomin masu shirya jarrabawa ta kasa NECO da WAECO da kuma NABTEB.
Sauran su ne kungiyar Shugabanni makarantu masu zaman kan su ta kasa NAPPS da kuma ANCOPSS da dai sauran su.
A dai makwan da ya gabata ne karamin ministan ilimi Emeka Nwajiuba ya sanar da cewar, an baiwa Najeriya zabin rubuta jarrabawar karshe ta kammala sakandire ta kasa daga watan Nuwanba zuwa Disamba.
.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *