July 16, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

An kara wa’adin rijistar NPower-sati biyu

1 min read

Gwamnatin tarayya ta kara wa’adin yin rijista karkashin shirin baiwa matasa aikin yi na N-POWER zuwa makwanni biyu ta kafar Internet.
An dai fara yin rijista ne a ranar Juma’a na watan jiya na Yuni ya yin da kare a jiya Lahadi 26 ga watan nan da muke ciki na Yuli.
Wannan na kunshe cikin sanarwar da mataimakiyar daraktan yada labarai na ma’aikatar dake kula da al’amuran jin kai da dakile Ifita‘ila da kuma cigaban al’umma Mrs Rhoda Ishaku Iliya ta fitar cewa, an kara lokacin ne don baiwa kowa dama don yin rijistar da kuma shawo kan matsalar da aka samu tun da fari.
Ka zalika Mrs Rhoda Ishaku Iliya ta ce kara lokacin ya zama wajibi kasancewar da dama daga cikin wadanda suka nemi yin rijista sun bayyana cewa su gamu da matsaloli a shafukan Internet akan ya sanya ma’aikatar ta kara wa’adin rufewar.
A saboda haka mataimakiyar darakatan ta yi kira ga matasa masu sha’awar shiga shirin su hanzarta wajen yin rijistar kafin lokacin ya kure.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *