April 23, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

An yanke wa ‘yan matan da ke amfani da TikTok hukuncin dauri a gidan kaso

2 min read

Wata kotu a Masar ta yanke wa wasu mata matasa masu dimbin
mabiya a kafar sadarwa ta TikTok hukuncin shekara biyu a gidan kaso
saboda samunsu da laifin yada rashin tarbiyya da kuma cutar da
al’adun iyalai.
An kuma yanke wa Haneen Hosssam da Mawda al Adham da wasu
matan uku da ba a bayyana sunansu ba tarar kusan dala dubu daya da
dari tara.
Rahotanni daga kotun sun ce matasan matan da iyalansu sun karbi
hukuncin kotun da matukar mamaki da rashin amana.
Hukuncin da aka yanke shi ne irinsa na farko da aka taba yanke wa
mata masu fada-a-ji a kafofin sada zumunta a kasar ta Masar,
wadanda hukumominta suka kaddamar da wani gangamin na nuna
rashin amincewa da wsu take-takensu a ‘yan makwannin da suka
gabata.
An kakkama wasu mutane, galibi matasan ‘yan mata, bisa zargin yada
wasu hotunan bidiyo da ba su dace ba. Abin da matan suka yada a
shafin intanet dai, yana nuna su ne sun ci ado da wasu tufafi irin na
gayu, suna kwakwayo ko ma tika rawar wata waka.
‘Yan gwagwarmayar kasar ta Masar sun fara wani gangami a shafin
intanet, suna neman a sakon matan da aka daure.
Da alama kuma hukumomin kasar sun yi tsayuwar daka wajen nuna
rashin amincewa da irin wannan halayya, wadda wani bangare na
jama’ar masu ra’ayin rikau su ma ba su yarda da ita ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *