July 18, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Anyi Dokar Kula Da Tsarin Tafiyar Da Harkokin Kudaden Gwamnati a Kano

2 min read

Yayin da gwamnatin jihar Kano
ta rage kasafin kudinta na bana da kimanin naira
biliyan 70 saboda mummunan tasirin da annobar cutar
coronavirus ta yi ga tattalin arzikin jihar, majalisar
dokokin jihar ta zartar da sabuwar dokar kula da tsarin
tafiyar da harkokin kudaden gwamnatin jihar.
Sai dai kungiyoyin rajin shugabanci na gari na cewa,
batun samar da doka lamari ne mai sauki, amma
aiwatar da ita shine kalubalen.
Samar da sabuwar alkiblar tafiyar da kudaden
gwamnati bisa tsarin dimokaradiyya na daga cikin
manufar sabuwar dokar a jihar Kano wadda tun a
shekarun baya aka samar da ita a matakin tarayya da
ma wasu jihohin Najeriya.
Shugaban masu rinjaye na majalisar dokokin jihar
Kano, Honarabul Kabiru Hassan Dashi, ya shaida wa
Muryar Amurka cewa, dokar za ta bai wa ma’aikatu da
gwamnatin jihar ka’idar yadda za su kashe kudadensu,
tare da yadda jihar za ta kasafta kudinta.
Yanzu haka dai kungiyoyin rajin shugabanci na gari sun
yi maraba da wannan doka, muddin dai za a bita sau
da kafa.
Daraktan kungiyar Organization for Community Civic
Engagement mai shelkwata a jihar Kano, Comrade
Abdulrazak Alkali ya ce suna fatan jami’an gwamnati,
da gwamnatin jihar za su aiwatar da dokar yadda ya
kamata.
To amma kwamishinan kudi da harkokin tattalin arziki
na jihar Kano Alhaji Shehu Na’Allah ya ce sun shirya
sosai domin aiki da dokar ka’in da na’in.
Tuni dai gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje
ya sanya hannu akan wannan sabuwar doka a karshen
makon da ya gabata kuma nan take ake sa ran za ta
fara aiki.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *