September 22, 2023

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Coronavirus a Najeriya: Mutum 65 sun kamu a Kano kuma yawan masu cutar ya zarce 40,000 a ƙasar

2 min read

Najeriya ta tabbatar da gano sabbin masu cutar korona 555 ranar
Lahadi, yawan mutanen da annobar ta shafa zuwa yanzu sun kai
40,532.
Cikin bayanan da take fitarwa a kullum, hukumar NCDC ta kuma
nuna cewa korona ta sake kashe mutum 2 cikin sa’a 24.
Alƙaluman sun kuma ce cutar ta kama mutum 65 a Kano, bayan
gano su ranar Lahadi. Ga alama wannan na daga cikin adadi mafi
yawa da aka samu na masu korona a jihar.
NCDC ta kuma nuna cewa masu korona 426 sun warke ranar Lahadi,
har ma an sallame su daga cibiyoyin kwantar da marasa lafiya da ke
faɗin ƙasar.
Hakan ya nuna cewa har yanzu akwai sama da masu cutar 22,000
da ke kwance suna jinya a Najeriya. Har yanzu Lagos ce jihar da ta fi fama da cutar a Najeriya, inda aka
sake gano masu korona 156 a ranar Lahadi.
Akwai jihar Ogun, can kuma an ba da rahoton kamuwar mutum 57, a
jihar Filato masu cutar korona 54 aka gano.
Sai Oyo, cutar ta kama mutum 53, a Binuwai 43. Abuja na da sabbin
masu cutar 30.
Haka zalika, korona ta kuma harbi mutum 18 a jihar Ondo, sai
mutum 16 a jihar Kaduna, kwana guda bayan ta kama wasu 50 a
jihar.
Jihohin Gombe da Akwa Ibom, an sake gano waɗanda korona ta
kama 13 cikin kowaccensu.
Sauran jihohin da aka sake gano masu korona ranar Lahadi, akwai
River mai mutum 12 da Ekiti mutum tara.
Jihar Osun, an sake gano mutum takwas, Cross River uku. A Borno
da Edo mutum bi-biyu sun sake kamuwa.
Akwai kuma mutum guda daga jihar Bayelsa, cewar hukumar NCDC.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *