June 13, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Godwill Akpabio ya lissafo sunayen yan majalisar da suka ci kudin kwangila-Delta

1 min read

Ministan kula da al’amuran yankin Niger Delta Godwill Akpabio ya bayyana sunayen ‘yan majalisar dake karbar aikin kwangila a hukumar ta NDDC.
Daga cikin sunayen wadanda suka karbi kwangilar akwai shugaban kwamitin dake kula da harkokin yanki Niger Delta na majalisar dattijai Peter Nwabaoshi.
A halin da ake cikin shi dai Sanata Nwabaoshi ya karbi aikin kwangila har guda 53 daga hukumar ta NDDC.
Wannan na kunshe cikin sanarwar da kakaki ga shugaban hukumar ta NDDC Anieta Ekong ya tabbatarwa jaridar Premium Times cewa ‘yan majalisar ne suke shan romun hukumar.
Sauran ‘yan majalisar dake karbar aikin kwangilar sun hada da Sanata Mattahew Urhoghide da yake da 6 sai Sanata James Manager da shima yake da 6 da kuma Sanata Samuel Anyanwu wanda yake da 19.
Sauran sune tsohon shugaban hukumar ta NDDC Nicholas Mutu wanda shima ya karbi kwangila 74.
Shi dai sanata Nicholas Mutu ya fi kowa samun aikin kwangila a hukumar ta NDDC kasancewar yana da kwangiloli daban-daban har guda 74.
Har ila yau a cewar Sanata Akpabio sauran ‘yan majalisar da suka karbi kwangilar sun fito ne daga majalisar wakilai a jihohin Ondo da Edo.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *