September 22, 2023

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Gwamnatin jihar jigawa ta soke hawan sallah baki daya

1 min read

Gwamnatin jihar Jigawa ta soke yin duk wasu bukukuwa na al’ada
bayan saukowa daga Sallar Idi.
Kwamishinan Lafiya kuma Shugaban kwamatin dakile yaduwar cutar
Covid-19 Dr, Abba Zakari Umar ne ya bayyana haka, jim kadan bayan
kammala taron tattaunwa da masu ruwa da tsaki kan lamarin.
Dr. Abba yace duk wanda zaije Sallar Idi dole ne sai ya sanya
takunkumin rufe baki da hanci, sannan kuma a bada tazara a
tsakanin mutane.
Kazalika Dr. Abba ya kuma kara da cewa bikin babbar Sallar zai
zamo ne kamar yadda aka yi na karamar Sallah, don kaucewa
yaduwar cutar corona Virus tsakanin mutane.
Wakilinmu Muhd Aminu Umar Shuwajo ya rawaito cewa, mahalarta
taron sun hada da sarakuna gargajiya, da kuma malamai sai yan
kwamatin yaki da cutar Covid-19 da sauran masu ruwa da tsaki.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *