June 13, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Kungiyar Shekarau Babes FC zata buga gasar rukuni na daya na NNL

1 min read

Tawagar Shekarau Babes FC, ta tabbatar da cewar zata shiga kana a dama da ita a gasar rukuni na daya wato Nigeria National league (NNL), na kakar 2021/2022.

Mai kungiyar , tsohon Gwamnan jihar Kano kana Sanatan Kano ta tsakiya Malam Ibrahim Shekarau ne , ya bayyana haka a daren Jumma’a lokacin da ya tattauna da mukarraban kungiyar a birnin tarayya Abuja

Malam Ibrahim Shekarau, ya shawarci mukarraban da su zakulo matasan ‘yan wasa masu hazaka don wakiltar kungiyar yadda ya kamata , kana ya yi alkawarin cewar da Zarar an samu hazikai 5 a cikin su , zai dau nauyin fitar da su zuwa kasashen Ketare don samun kungiyoyi na kasashen waje.

A sanarwar da kakakin tawagar Ahmad Babandi Gama, ya sakawa hannu aka rabawa manema labarai, Malam Shekarau ya ce , kowa ya san muhimmancin da harkokin wasanni yake dashi wajen bunkasa matasa da samar musu da aiyyukan yi , don haka a shirye yake a koda yaushe don bada gudummowa a bangaren.

Sanatan Kano, na tsakiya ya kuma godewa jagororin kungiyar da ‘yan wasa ,duba da lokacin su da himma da suke bayarwa a kan kungiyar a koda yaushe ba tare da gazawa ba , tare da umartar su da su zama jakadu nagari a koda yaushe.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *